Ana zaben yankuna a kasar Kamaru
December 6, 2020Talla
Sama da shekaru 20 ne dai kundin tsarin mulkin ya bayar da damar zaben na yankuna, to sai dai a wannan karon ne ake iya cewa 'yan kasa za su gani.
A karshen shekarar da ta gabata ne, Shugaba Paul Biya, ya yi alkawarin zaben a kokarin kwantar da wutar rikicin ‘yan aware da ke ruruwa a yankin renon Ingila na kasar.
Manufar hakan kuwa shi ne domin bai wa yankin karin ikon mulki musamman ma a kan batutuwan da suka shafi al’umomin da ke zaune a cikinsa.
Sai dai kuma a bayyane yake, galibin mazauna yankin dai ba su da kwarin gwiwa a wannan zabe na yau.