Ana zanga-zangar kyamar sabon firaministan Faransa
September 7, 2024Dubban mutane sun yi fitar dango a kan manyan titunan Faransa domin nuna adawa da nadin Michel Barnier a matsayin sabon fiministan kasar.
'Yansanda sun bayyana cewa a birnin Paris kadai mutane kusan dubu 26 ne suka fantsama kan tituna sai dai kuma wasu na ikirarin adadin ya fi haka.
Michel Barnier ya zama sabon Firaministan Faransa
Akwai kuma kananan gangami da aka rika gudanarwa a wasu garuruwan na Faransa ciki har da Nantes da Marseille da kuma Starasbourg.
Takaddama a kan ziyarar Tinubu cikin wani sabon jirgin sama zuwa Faransa
A ranar Alhamis na makon da ya gabata ne shugaban kasar Emmanueal Macron ya zabi Michel Bernier mai shekara 73 a matsayin sabon firaminsta bayan zaben majalisa da ya gudana a watan Yuli wanda kuma bai yi wa Macron din dadi ba.
Sabon firaminstan ya na da aikin tabbatar da samar da gwamnati da ta kunshi dukkan bangarorin siyasa domin kauce wa sabanin siyasa da ake fama da shi.