1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza

August 10, 2024

Bangarori dabam-dabam na zargi Isra'ila da aikata kisan gilla a Zirin Gaza, bayan harin ta sama da ta kai kan wata makaranta ya yi sanadin rayukan mutane fiye da 100.

Isra'ila ta kai hari kan makarantar da 'yan gudun hijira ke samun mafaka a Gaza
Isra'ila ta kai hari kan makarantar da 'yan gudun hijira ke samun mafaka a GazaHoto: Omar Al-Qattaa/AFP/Getty Images

Babban jami'in diflomasiyya na kungiyar Tarayyar Turai, EU Josep Borrell ya nuna kaduwarsa kan harin da Isra'ila ta kai kan makarantar Al-Tabeen. Jami'in ya jadadda cewa, cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta shi ne kadai mafita na dakatar da kisan fararen hula da ma ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Karin bayani: Isra'ila ta kai hari kan wata makaranta a Gaza

A sakon da ta wallafa a shafinta na X da aka fi sani da Twitter a baya, mai bayar da rahoto ta mussaman ta Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkin dan Adam a Gaza, Francesca Albanese ta ce Isra'ila na aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a lokaci guda, inda ta kai hari kan makaranta da asibiti da ma sansanin 'yan gudun hijira.

Albanese ta kuma kara da cewa, Isra'ila na kai wadannan hare-hare ne da makaman Amirka da kuma kasashen Turai. Sai dai Isra'ila da ta dade tana sukar jami'ar da ayyukanta, kana ta yi watsi da zargin tana mai cewa na kazan kurege ne.