MDD ta zargi China da cin zarafi a Xinjiang
September 1, 2022Talla
Rahoton ya ce zargin nau'ikan azabtarwa ko musgunawa da munin yanayin wurinj tsare mutane, tabbaci ne na irin wulakancin da gwamnatin Bejin ke aiwatarwa kan musulmai tsirarru.
Kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch da sauran kungiyoyi sun dade suna zargin China da tsare 'yan kabilar Uygur fiye da miliyan daya a yankin Xinjiang. Sabon rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce lamarin na bukatar kulawar gaggawa daga gwamnati, hukumomin Majalisar da tsarin kare hakkin bil adama, da ma sauran kasashen duniya baki daya.