Zargin Denmak da laifin leken asiri
June 1, 2021Kasashen Turai da dama ne suka nemi kasar Denmak, da ta fitar da kanta daga cikin zargin tatsarwa Amirka baiyanan sirri na wasu shugabanin kasashen Turai da aka ce tayi. Wannan na zuwa ne, bayan da wani bincike ya bankado yadda Denmak ta kwashi shekaru akalla bakwai tana wa Amirkan leken asiri.
Daga Ma'aikatar leken asirin Denmak ake zargin ana aikin tsatsar bayanai daga wayoyin tarho na wasu daga cikin shugabanin yankin na Turai ana mika ma Amirka. Jamus da Faransa na daga cikin wadanda lamarin ya shafa, sun kuma baiyana takaici kan lamarin musanman ganin kusancinsu da Denmark, daga bisani su nemi Amirka ta yi kokarin wanke kanta dangane da wannan batu. Tuni ita gwamnatin kasar ta Denmak ta sanar da kafa kwamiti don soma bincike, a gano inda aka aikata ba daidai ba a batun da ya harzuka kasashen na Turai.