Zargin Mahamadou Issoufou da laifin cin amanar kasa
September 19, 2022Kawancen kungiyoyin farar hula na M62 a jamhuriyar Nijar ne suka yi kira ga gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da ta gurfanar da Mahamadou Issoufou a gaban kuliya a bisa zarginsa da cin amanar kasa, kan batun kwangilar shimfida layin dogo da ma girke sojojin ketare a kasar.
Kawancen kungiyoyin na M62 wanda ya kunshi kungiyoyin farar hula da na kwadago, ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a taron gangamin da ya shirya a karshen makon da ya gabata. Kawancen na zargin tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou da cin amanar kasa ta hanyar girke sojojin ketare a kasar ba da izinin majalisa ba, da kuma bai wa kamfanin Bolore na Faransa kwangilar shimfida layin dogo daga Yamai zuwa Dosso ba a kan ka’ida ba.
Tuni dai wannan batu ya haifar da sabani a tsakanin sauran kungiyoyin farar hula wadanda ba sa cikin kawancen na M62. Kawancen na M62 ya ce, idan har mahukuntan Nijar ba su gurfanar da tsohon shugaban kasar Alhaji Mahamadou Issoufou a gaban kuliya ba, to a shirye suke su shigar da karansa a gaban wata kotun kasa da kasa domin cimma burinsu.