1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP na zargin shugaba Buhari da kama karya

Ubale Musa/YBOctober 19, 2015

Muhawara ta barke a tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da kuma PDP ta adawa a Najeriya inda ta ce shugaban kasar ya kama hanyar kama-karya, da mai da 'yan bangaren jam'iyyarsa 'yan lele.

Niger Buhari Issoufou
Shugaba Muhammadu BuhariHoto: DW/M. Kanta

Hankali ya tashi kuma zuciya ta yi baki a cikin jam'iyyar ta adawa da ta kalli gayyatar shugaban marasa rinjayen jam'iyyar a cikin zauren majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio bisa zargin satar dubban miliyoyin Nairori.

Hukumar yakar hancin kasar ta EFCC dai ce ta ce Akpabio na da abu na gayyata bayan da wani lauyan da ke a Abuja ya shigar da korafin da a cikinsa ya zargi Akpabio da sace tsabar kudi har Naira Miliyan dubu 108 mallakin Jihar Akwa Ibom.

To sai dai kuma ‘yan sa’oi da sakin Akpabio jam'iyyar ta PDP ta zargi shugaban kasar da kama karya a zuciya da aiyyukan da yake yi yanzu. Tuni dai a tunanin PDP Buhari ya zartar da hukuncin laifi kan ‘yan PDP a fadar kakakinta Oliseh Metuh, sannan kuma ya fara aiwatar da laifin yanzu farawa daga jigo na adawar majalisar.

PDP dai ta ce ba za ta lamunci matakin gwamnatin kasar da ke neman rushe adawa da kuma dora kasar a bisa tafarkin kama karya yanzun ba.

Rotimi Amaechi tshohon gwamnan Rivers da ake zargi da wadaka da dukiyar jiharsaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Akwai korafi akan ‘ya’yan APC a ko'ina amma kuma shugaba Buhari ya zabi kawar da idanunsa tare da maida hankali akan ‘yan PDP abun kuma da a cewar Metuh ya saba da hankali kuma ke fitar da hali na Buharin kowa ya gani.

“Akwai korafi akan tsohon gwamnan Rivers akwai korafi akan tsohon gwamnan Legas da korafi akan tsohon gwamnan Ekiti, amma me ka yi duk ka dauke su ka saka musu da ministoci. Wasu kuma da matsalolinsu ke gaban kuliya ka basu tukwicin tsayawa jam'iyyarka takara ta gwamna a jihohinsu. Maganarmu ita ce gaiyyaci duk wani dan jam'iyyarmu da ka zarga da kokarin halin bera , amma kuma ka isar da gaiyyatar ga ‘ya‘yan jam'iyyarka da mutane suka bada ingantacciyar shaidar hannunsu a cikin maganar sata, kar ka nuna fifiko”

kokari na nunin fifiko ko kuma kokari na yakar hanci dai sabon korafin na jam'iyyar PDP na nuna irin tsaka mai wuya ta shugaban kasar da ke da alkawarin yakar hanci amma kuma ke da jan aikin banbansa tsakanin yakin da bakar guguguwar siyasar da ke turnuku cikin kasar a halin yanzu.

Babbar kotun Abuja NajeriyaHoto: DW/U. Musa

PDP dai ta ce na shirin kama hanyar neman alkalanci a wajen kasar in har Buharin ya dora a cikin yakin da PDP ke yi wa kallon da biyu.

To sai dai kuma in har tana shirin baki da baci a tunanin PDP ga ofishin kula da kare muradu na Buharin a APC korafin ba shi da hujjar gaske a fadar Malam Muhammad Labbo da ke zaman kakaki na cibiyar a Abuja.