SiyasaAfirka
Ana zargin sace abinci a yankin Tigray
June 18, 2023Talla
An fara binciken bayan da manyan kungiyoyin agaji na USAID da kuma hukuumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya suka dakatar da kai dauki bayan da aka gano abincin da suka samar a kasuwannin kasar ana sayar da su. Binciken ya gano cewar an sace sama da tan dubu 7 na alkama da kuma litar mai sama da duubu dari biyu.
Sama da mutum miliyan biyu ne suka dogara da wannan dauki a kasar da ke zama ta biyu a yawan al'umma a nahiyar Afirka.