1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargin sojoji da kisan fararen hula a Nijar

Gazali Abdou Tasawa M. Ahiwa
December 27, 2022

A Jamhuriyar Nijar, hukumar kare hakkin dan Adam CNDH ta gabatar da rahoton bincike kan zargin da aka yi wa jami'an tsaron kasar na kisan fararan hula a kauyen Tamou.

Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Rahoton ya tabbatar da mutuwar mutane 11 da kuma jami'an tsaro biyu a cikin lamarin. Sai dai wasu kungiyoyin farar hula sun nuna rashin gamsuwarsu da rahoton tare da bayyana bukatar gudanar da wani bincike mai zaman kansa kan batun. A ranar 24 ga watan Oktoban da ya gabata bayan wani harin da ‘yan ta'adda suka kai kan jami'an tsaro a yankin na Tamou, sojojin Nijar din suka kai farmakin martani kusa da mahakar zinariyar gargajiya ta kauyen wacce suke zargi da kasancewa mabuyar 'yan ta'adda.

A wancan lokaci wasu kungiyoyi sun ruwaito cewa sojojin sun kashe daruruwan fararan hula a  farmakin wanda gwamnati ta ce mutum 11 suka mutu wasu 25 suka jikkata. Lamarin da ya haifar da cece-kuce e kasar. A kan haka ne hukumar ta CNDH ta gudanar da binciken hadin gwiwa da wasu hukumomi da kungiyoyin fararan hula.

Hukumar ta CNDH ta kuma ce gwamnati ta sha alwashin biyan diyya ga duk mutanen da suka jikkata da ma iyalan wadanda suka rasa ransu a harin. Sai dai kungiyar M62, daya daga cikin kungiyoyin fararan hula da suka bukaci ganin an gudanar da bincike kan wannan lamari, ta bakin magatakardanta Malam Sanoussi Mahaman ta ce ba ta gamsu ba dari bisa dari da rahoton hukumar ta CNDH.

Yanzu dai abin jira a gani, shi ne ko wannan rahoton bincike na hukumar ta CNDH zai kawo karshen muhawara kan wannan lamari na Tamou ko kuma wasu kungiyoyin kasa-da-kasa masu zaman kansu za su shigo cikin maganar domin gudanar da nasu bincike kamar yadda wasu kungiyoyin farar hula na kasar ta Nijar suka bukata.