1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ANC mai mulkin Afirka ta Kudu na fuskantar janyewar masoya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 24, 2024

Shugaba Cyril Ramaphosa da jam'iyyarsa na fuskantar janyewar magoya baya da kuma bakin jini sakamakon tarin zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin iya mulki da suka yi wa gwamnatinsa katutu

Hoto: Denis Farrell/ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Jam'iyya mai mulkin kasar Afirka ta Kudu ANC ta kaddamar da fara yakin neman zaben kasar da za a gudanar a ranar 29 ga Mayu mai zuwa, a daidai lokacin da kasar ke kara tsunduma cikin halin tabarbarewar tattalin arziki mafi muni a tarihinta.

Karin bayani:Julius Malema ya zargi jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu da jefa kasar cikin tasku

Shugaba Cyril Ramaphosa da jam'iyyarsa na fuskantar janyewar magoya baya da kuma bakin jini sakamakon tarin zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin iya mulki da suka yi wa gwamnatinsa katutu.

Karin bayani:Putin ya fasa halartar taron BRICS a Afirka ta Kudu

Dubban magoya bayan ANC din ne dai suka yi dafifi a filin wasa na birnin Durban, don shaida kaddamar da yakin neman zaben inda shugaba Cyril Ramaphosa ya zayyano manufofin da suka sanya a gaba don cimmawa idan sun sake samun nasarar zaben.