Angela Mekel ta samu lamnar yabo
September 17, 2014![Bundestag Generaldebatte 10.09.2014 Merkel](https://static.dw.com/image/17911915_800.webp)
Talla
Kyautar ta yawan kuɗaɗe tsaba dala dubu dari biyu saboda amincewarta cewar Jamus na da hannu cikin ta'asar da gwamnatin 'yan Nazi ta Hitler ta aikata a duniya,na zaman wani babban ci gaba a gareta,.
Merkel ita ce mutun na 12 da ta samun wannan kyauta wacce aka fara ba da ta tun shekarun 1990. Alƙalan da suka tantanceta, sun ce a cikin jawaban da take yi, a kowane lokaci Merkel ta kan ambato aikin na asha da 'yan Nazi suka aikata tare da nuna takaicinta.