Angela Merkel a Amurka
January 12, 2006Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta kama hanyarta ta zuwa kasar Amurka a yau alhamis,cikin wata ziyara da ake ganin zata sabunta dangantaka tsakanin Jamus da Amurka bayan tsamin dangantaka tsakanin George Bush da tsohon shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schroeder.
Merkel a ziyararta ta farko zuwa Amurka tun darewa shugabancin Jamus a ranar 22 ga watan nuwamban bara,zata gana da jamian kasar Jamus dana Amurka su 180 a ofishin jakadancin Jamus dake birnin Washington,a gobe jumaa kuma zata gana da shugaba Bush,inda zasu tattauna batun nukiliya na Iraqi,yayinda a yau din nan kuma ministocin harkokin wajen kasashen Jamus,Burtaniya da Faransa suke ganawa domin tattauna martani da zasu bayar,bayan komawar Iran aiyukanta na binciken nukiliya.