1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel na ziyara a Japan

February 4, 2019

A karo na biyar a mulkinta, Angela Merkel ta Jamus na wata ziyarar kyautata ci gaba tsakanin kasarta da Japan. Ziyarar dai ta kwanaki biyu ce.

Bundeskanzlerin Merkel in Japan
Hoto: Reuters/F. Robichon

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta isa kasar Japan a wannan Litinin a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ta kai kasar.

Angela Merkel za ta gana da Firaministan Shinzo Abe na Japan da wasu manyan masu hannu cikin harkokin kasuwanci gami da daliban jami'o'i.

In an jima ne dai Merkel za ta gana da Firamnista Abe, inda ake kyautata zaton za su zanta kan batun kasuwanci marar shinge da batun Nukiliyar Koriya ta Arewa da ma ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.

Wannan ne dai karo na biyar da Angela Merkel ke ziyartar Japan a matsayin shugabar gwamnati.

Akwai ma dai karin wasu batutuwan da shugabannin biyu za su tabo a kwanakin biyu, musamman batun ci gaban fasahar zamani.