Angela Merkel ta buɗe taron duniya kan tattalin tattalin arziki
January 25, 2007Talla
SGJ Angela Merkel ta bude taron kasashen duniya kan tattalin arziki a garin Davos na kasar Switzerland, inda ta yi wani jawabi mai muhimanci akan shirye shiryen Jamus a matsayin ta na shugabar kungiyar G-8 da ta KTT. Merkel ta ce a wa´adin shugabancin Jamus na kungiyar EU na tsawon watanni 6 za´a yi aiki a kan taken karin ´yancin akan sabon yanayi na tsaro. A game da harkar kasuwancin duniya kuwa Merkel cewa ta yi kasashen dake bin manufofin kariya don yaki da hadakar manufofin kasuwancin duniya wato globalisation suna kan wata hanya karkatacciya. SG ta Jamus ta ce ana bukatar sassauci daga dukkan sassan da abin ya shafa don sake farfado da shawararin kan cinikaiya ta duniya wadanda suka cije. A bana shugabanni da manyan ´yan kasuwa kimanin dubu 2 da 500 ke halartar taron na Davos.