1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta yaba wa matakan tsimi na ƙasar Italiya

January 11, 2012

Jamus da Italiya na fatan aiki kafaɗa da kafaɗa domin tunkarar matsalar ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin euro.

German Chancellor Angela Merkel speaks during a news conference after talks with Italian Prime Minister Mario Monti at the Chancellery in Berlin, January 11, 2012. REUTERS/Thomas Peter (GERMANY - Tags: POLITICS)
Ganawar Angela Merkel da Firaministan Italiya Mario MontiHoto: Reuters

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatarwa da Firaministan Italiya Mario Monti cewa ƙasar za ta ci moriyar matakan tsimin da ta ɗauka domin ta da komaɗar tattalin arzikin ƙasar. Shugabannin biyu sun gana yau a birnin Berlin domin gano bakin zaren magance rikicin kuɗin da ya dabaibaye ƙasashe 17 masu amfani da takardun kuɗin euro. Merkel ta baiyana yabo da girmamawa ga Firaministan Italiyan Mario Monti ta na mai cewa ta yi imani ƙasar za ta girbi alheri daga matakan tsimin da ta ɗauka. A nasa ɓangaren Firaminista Monti ya baiyana fatan kasuwannin hada hadar kuɗaɗe za su yi la'akari da irin sadaukarwa da ƙasar ta yi na ɗaukar waɗannan matakai domin samun cigaba mai ma'ana.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita:Zainab Mohammed Abubakar