Angela Merkel ta yaba ziyararta a Ƙasar Sin
February 4, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana ziyarar rangadi ta kwanaki uku da ta kai ƙasar Sin da cewa ta yi aramashi matuƙa. Sai dai kuma ta baiyana damuwa akan matsayin haƙƙin bil Adama a ƙasar. Bayan ganawa da manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da Firimiya Wen Jiabao da kuma shugaban ƙasa Hu Jintao, Angela Merkel ta kuma tattauna da shugaban gundumar Guangdong. Ta baiyana farin ciki da ziyarar tana mai cewa " Ta ce sabon al'amari shine cewa China a shirye take ta yi aiki da tarayyar Turai da kuma taimakawa ta fannoni da dama. Za mu ƙara tattauna cikakkun bayanai akan wannan a nan gaba".
A nasa ɓangaren shugaban China Hu JIntao yace ƙasashen biyu na fatan ƙarfafa dangantaka da fahimtar juna a tsakaninsu. Shima Firimiyan ƙasar ta Sin Wen Jiabao ya tabbatarwa da shugabar gwamnatin ta Jamus amannar Beijin akan takardun kuɗin bai ɗaya na euro. Yana mai baiyana ƙudirin China na taimakawa wajen shawo kan matsalar bashi da ta dabaibaye ƙasashe masu amfani da kuɗin na euro.
A waje guda kuma 'yan sanda sun hana wani fitaccen lauya mai fafutukar kare haƙƙin bil Adama halartar liyafar da aka shirya a ofishin jakadancin Jamus dake Beijin. An dai gaiyaci Mo Shaoping ya halarci liyafar wadda shugabar gwamnati Angela Merkel ta kasance babbar baƙuwa.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi