Angela Merkel za ta yi jawabi kan kyamar Yahudawa
September 11, 2014Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta yi jawabi a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus a ranar Lahadi kan taron gangami na nuna adawa da kyamar da ake nuna wa Yahudawa musamman ta kalaman batanci da ake nuna musu da ma farmaki wanda shi ne sanadin rura wutar rikici na baya bayan nan a Zirin Gaza.
Wannan taro kuwa na zuwa ne shekaru 75 da barkewar yakin duniya na biyu, wanda a lokacinsa Jamusawa masu akidar Nazi suka kashe Yahudawa miliyan shida, laifin da ya zamo wani abu da ake alakanta kasar da aikata wani abin kunya cikin tarihinta.
Taron da za a yi a gaban kofar nan mai tarihi ta Brandenburg a birnin Berlin zai dauki taken "A tashi tsaye: kyamar Yahudawa har abada". Zai kuma zo ne a daidai lokacin da za a gudanar da babban taron Yahudawa na WJC a fadar gwamnatin kasar.