1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angola: Mutane 17 sun mutu a filin kwallo

Salissou Boukari
February 11, 2017

Ma'aikatar 'yan sandan kasar Angola ta ce turereniya da ta afku a filin kwallon kafa na birnin Uige da ke arewacin kasar a lokacin da masu sha'awar kwallon kafa suka nemi shiga filin ta yi sanadin rasuwar mutane.

Angolanische Fußballclubs trainieren in Brasilien
Hoto: CRUZEIRO ESPORTE CLUBE

Filin kwallon dai mai daukar mutun 12,000 ya cika makil a daidai lokacin da daruruwan masu sha'awar kallon kwallon suka nemi shiga da karfi. Shugaban kungiyar kwallo kafa ta Santa Rita ya dora alhakin hakan kan jami'an tsaro da suka bari har mutanen suka iso kusa da kofar shiga duk kuwa da cewa filin kwallon ya cika makil.

An dai sha samun irin wannan hadari a filayen kwallo sakamakon turereniya, inda a shekarar ta 2001 mutanen 127 suka mutu a filin kwallon kafa na Accra a kasar Ghana, yayin da 2009 irin haka ta faru a birnin Abija na kasar Cote d'Ivoir, inda mutane 19 suka rasu a wani wasa da kasar ta buga da Malawi.