1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angola ta samu lu'u-lu'un da ya zarta na kowacce kasa

July 27, 2022

Masu hakar ma'adanai a Angola sun ce sun hako wani lu'u-lu'u mai ruwan hoda da aka kwashe daruruwan shekaru ba a taba samun irinsa a duniya ba, matakin da zai kara wa kasar karfin arziki.

Angola - Historischer Diamant gefunden, 170 Karat
Hoto: LUCAPA DIAMOND COMPANY LIMITED/AFP

Kamfanin Lucapa mallakin kasar Ostireliya da ke aikin hakar ma'adanan ne ya sanar wa da hukumomin Angola a Larabar nan cewa ya hako lu'u-lu'un mai nauyin carat 170 da kuma aka yi wa lakabi da Lulo Rose. 

Ana fatar lu'u-lu'un mai ruwan hoda zai kawo wa Angola makudan kudade, domin kafin yanzu, rahotanni sun ce babban lu'u-lu'u mai tsada a duniya shi ne mai nauyin carat 59.6 wanda aka sayar a shekarar 2017 a birnin Hong Kong a kan kudi Euro miliyan 70. To sai dai kuma akwai yiwuwar nauyin lu'u-lu'un na Angola ya ragu daga nauyinsa na carat 170 bayan an wanke shi.