1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angola: Za a tuhumi 'yar shugaban kasa

Ramatu Garba Baba
February 3, 2020

Shugaban Joao Lourenco a Angola ya karyata batun shiga yarjejeniya da 'yar tsohon Shugaba Isabel dos Santos don dawo da kudaden gwamnati da ta karkatar.

João Lourenço, Angola Präsident
Hoto: Getty Images/M. Spatari

Wani bincike da aka gudanar ne ya nunar da almundahanar da 'yar tsohon shugaban kasar Angola Isabel dos Santos ta yi na karkatar da kudaden gwamnati zuwa ajiyarta a kasashen Turai. Rahoton binciken ya bayyana yadda Isabel dos Santos, ta yi amfani da mukamin mahaifinta wajen azurta kanta.

Matar da aka ce ita ce ta fi ko wacce mace yawan dukiya a nahiyar Afirka, ta nemi ta dawo da tarin dukiyar da ake zarginta da wawashewa.

An dai ci gaba da yada jita-jitar cewa ta shiga yarjejeniya da gwamnati don dawo wa kasa da kudaden da ta wawushe, amma a wata tattaunawa da tashar DW, shugaban kasar Joao Lourenco, ya karyata batun wata yarjejeniya da ita, inda ya ce dole a bar doka ta yi aikinta.

Ya ce kasancewar akwai lokacin da aka tanadar ga duk wanda ya san ya ci kudin kasa na watanni shida da ya dawo da kudadden, saboda haka wa'adin ya wuce wa Isabel dos Santos, a don haka babu batun a shiga wata yarjejeniya da ita in ji shugaban.