1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAngola

Angola za ta fice daga OPEC saboda rashin jituwa

Abdourahamane Hassane
December 21, 2023

Angola ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, sakamakon rashin jituwa kan kason da aka ware mata ta hako na man.

Hoto: Maneesh Bakshi/AP Photo/picture alliance

 Angola ta ce yazuwa yanzu ba ta da wani tasiri a kan kason,da aka ware ma ta, tana mai cewa lokaci ya yi da za ta kara yawan man da take hakowa domin cimma manufofinta. Ministan albarkatun kasa, na man fetur da iskan gas na Angolar Diamantino  Azevedo ya ce idan suka ci gaba da zama a cikin kungiyar ta OPEC, za su fuskanci koma baya. OPEC ta kafa kason ganga miliyan daya da dubu11 ga Angola a kowace rana, yayin da Angolar ke son haura wannan kaso da ganga miliyan daya  da dubu 18.