Annalena Baerbock: Fafatukar neman ofishin shugaban gwamnati
April 19, 2021Shin waye zai gaji kujerar shugbancin gwamnatin Jamus bayan zaben watan Satumba mai zuwa? Wannan na zama tambaya mai tasiri tsakanin jam'iyyun siyasa na Jamus, amma ga jam'iyyar kare muhalli ta The Greens, ta tsayar da 'yar takara mace Annalena Baerbock domin yin takarar neman kujerar shugabancin gwamnatin ta Jamus.
Tun daga farawa babu wata tantanma, Annalena Baerbock wadda take jagorancin jam'iyyar ta the Greens tun shekara ta 2018 kuma mamba a majalisar dokoki ta Bundestag ake gani za ta yi takara wa jam'iyyar. 'Yar siyasar daga Hanover ta kasance mai jawabin da ke jan hankalin mutane.
Ita dai Annalena Baerbock ta kasance tana jagorancin jam'iyyar kare muhalli tare da Robert Habeck, kuma Baerbock 'yar shekaru 40 da haihuwa nan da nan ta samu karbuwa da fitowa fili. Robert Habeck yana cikin wadanda suka fara mubayi'a ga wannan takara tare da nuna tasirin zabin da jam'iyyar a wannan yanayin da ake ciki.
"Kafin kafa gwamnati akwai yakin neman zabe. Kuma wannan yakin neman zaben a karon farko jam'iyyar kare muhalli ta tsayar da mace, Annalena Baerbock, ta yi mata takara bisa neman shugabancin gwamnati."
Ita ma kanta Annalena Baerbock da ake gani mai kazar-kazar ta nuna juriya da sanin ya kamata musamman game da muradun kare muhalli a yanayin da duniya ke ciki, ta yi kira da daukacin al'umma bisa samun nasararta baki daya.
"Muna bukatar samun sauye-sauye da adalci a kasa, inda yara da 'yan makaranta za su samu wurare gwanin sha'awa. Kasa da ke nuna kulawa da amfani da ma'adanai domin kula da al'umma. Kasa wadda take aiki da zamani domin inganta rayuwar al'ummarta. Kasa wadda take bude kofofinta ga mutane dabam-dabam, kan abin da suka yi imani da kare dimukuradiyya. Jamus da take da tasiri a nahiyar Turai."
Sannan Annalena Baerbock ta nuna muhimmanci kan kasa da take kare muhalli da kirkiro hanyoyin inganta rayuwa nan gaba cikin walwala da cikekken tsaro. Farfesa Thorsten Faas masanin harkokin siyasa a jami'ar Free University da ke birnin Berlin ga abin da yake ganin bisa matakin jam'iyyar kare muhalli ta Jamus kan tsayar da mace domin neman shugabancin gwamnati.
"Abin da kuri'ar jin ra'ayin mutane na baya-baya ya gano shi ne akwai kankankan da Annalena Baerbock wannan a gare ni samun karbuwa ne, kuma idan aka duba gaba daya, ita ce kadai mace da aka tsayar takarar kujerar shugabancin gwamnati. Mun ga yadda Angela Merkel, kasancewarta mace, ya karawa mata karbuwa, saboda musamman ga mata masu zabe da haka yake cikin abin da suke dubawa. Wannan ka iya zama wata dabara."
Yayin wata hira da tashar DW a farkon wannan shekara Annalena Baerbock ta nuna jin dadi da sabon Shugaba Joe Biden na Amirka ya mayar da kasar karkashin yarjejeniyar kare muhalli ta birnin Paris.
Tuni dai jam'iyyar SPD da ke cikin kawancin gwamnatin Jamus ta tsayar da Olaf Scholz ministan kudi kana mataimakin shugaban gwamnati a matsayin wanda zai yi takara na neman shugabancin gwamnati ga jam'iyyar.