1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan da Merkel sun jagoranci bukin bude sabon ofishin MDD a Bonn

July 11, 2006
Babban sakataren MDD Kofi Annan da SGJ Angela Merkel sun kaddamar da bukin bude sabon ofishin MDD a kusa da tashar DW dake nan Bonn tsohon babban birnin tarayyar Jamus. Daga yau talata hukumomin 12 na MDD ne zasu tare a wannan gini wanda ya kasance tsohon ofishin ´yan majalisar dokoki bayan an yi masa gagarumar kwaskwarima. Tun a cikin shekarar 1996 Bonn ya samu take na zama birnin MDD. A lokacin bukin bude sabon ofis din mista Annan ya ce zai goyawa Jamus baya a kokarin ta na samun dauwamammiyar kujera a kwamitin sulhun MDD. Bayan ganawar da suka yi da Merkel, Annan ya ce Jamus na taka muhimmiyar rawa a cikin MDD, a saboda haka ba´a nuna adalci ba idan kasashe dake ba da gagarumar gudummuwa ga Majalisar ta Dinkin Duniya ba su samun cikakken wakilci a kwamitin sulhu ba.