Annan yayi kira da kafa wata sabuwar runduna ga kudancin Libanon
July 18, 2006Talla
Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kira da a kafa wata babbar runduna mai cikakken kayan aiki wadda zata daidaita al´amura a kudancin Libanon. Annan ya ce rundunar zata bawa gwamnatin Libanon karin lokacin kwance damarun dakarun Hisbolah. Annan ya yi wannan kira a ne a tattaunawar da yayi da shugaban hukumar KTT Jose Manuel Barroso a birnin Brusssels. Babban sakataren na MDD ya nuna halin ko-in kula da adawar da Amirka da Isra´ila ke nunawa girke irin wannan runduna a Libanon. Annan ya ce yana sa rai kasashen Turai zasu ba da gudummawar dakaru ga wannan runduna da ake shirin kafawa da zummar kawo karshen fadan da ake gwazawa tsakanin Isra´ila da Hisbollah tare da hana wannan rikici yaduwa a yankin GTT gaba daya.