1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin samar da allurar rigakafin cutar corona

December 1, 2020

Kamfanonin hada magunguna na ci gaba da kokarin wajen samar da rigakafin cutar corona duk kuwa da cewar kamfanin na Jamus BioNTech da takwaransa na Amirka Pfizer sun samar da rigakafin.

Deutschland Ciovid-19 Impfstoff von BionTech
Hoto: Laci Perenyi/picture alliance

Wasu kamfanonin harhada magunguna sun yi nisa wajen aikin samar da rigakafin cutar corona, haka ma abin yake da wasu masana kimiyya da ke aiki na kashin kansu kan wannan batu da duniya ta zaku ta ga an kai gabar da rigakafin zai shiga kasuwa.

Kamfanin Moderna da ke hada magunguna dai shi ne na baya-bayan nan da ya samu nasarar yin rigakafin cutar ta corona, kuma tuni ma ya mika bukatarsa ta samun sahalewar hukumar kula da magunguna da abinci ta Amirka da takwararta ta nahiyar Turai don fara amfani da rigakafin.

Baya kuma ga manyan kamfanoni da ke kokari wajen samar da rigakafin, masana kimiyya ma dai na nasu kokarin wajen ganin sun ba da gudumawa wajen samar da rigakafin, guda kuma daga cikinsu shi ne Michael Piontek, kuma a nasa bangaren yana kokari ne wajen ganin rigakafin da zai fidda za ta sha banban da sauaran da nan gaba za a fidda ko ma aka rigaya aka fidda musamman ma ta fuskar farashi amma kuma batun sahihanci na gaba da komai kamar yadda ya nunar.

Karin bayani: Moderna na neman izini kan allurar corona

"Abu na farko shi ne a tabbbatar da sahihancin rigakafin ta hanyar la'akari da da irin sinadarin aka yi amfani da shi, sannan a tabbatar cewar za ta yi aiki sosai ba tare da ta yi illa ga dan Adam ba kana a iya samar da shi ga kowa da kowa."

Michael Piontek, shugaban kamfanin Artes BiotechnologyHoto: DW/N. Martin

Irin tsarin da Piontek ya dauka kusan za a iya cewa ya sha banban da na manyan kamfanonin hada magunguna, don ya kan sayar da fasahar da ya kirkira ta magunguna da kuma rigakafi ga kasashen da ke nahiyar Asiya wanda wasu daga ciki suka samar da rigakafin cutar nan ta Hepatitis B daga irin fasahar da ya kirkira, kuma za a iya amfani da irin wannan tafarki wajen samar da rigakafin corona ba tare da an kashe kudi da yawa ba.

"Za mu iya samar da rigakafin a farashi mai rahusa, idan aka yi la'akari da rigakafin da aka samar a baya, akwai yiwuwar wannan din mu samar da shi kuma a iya sayar da shi a kan farashin da bai euro guda ba kuma duk da cewar kudin ba yawa, za ta iya yin aikin da sauran ma za su yi. Mu ba mu damu a ce sai mun samu kudi da yawa daga abin da muka yi ba don tun kafin a kawo ga wannan gaba mun samu abin da muka samu."

Karin bayani:Turai da Amirka za su amince da rigakafin corona

To sai dai duka da wannan kokari da yake yi, lamarin zai iya daukar lokaci kafin a gama gwaje-gwajen da suka kamata musamman ma kan bil Adama, kuma ga irin tsarin da kamfaninsa ke da shi a iya cewa bai da karfin da zai iya kammala wannan aiki. Hakan ne ma ya sanya shi gama gwiwa da manyan kamfanoni na hada magunguna a nahiyar Asiya don cimma nasarar da aka sanya a gaba, kuma baya ga Asiya, Piontek ya ce zai shiga nahiyar Afirka domin kasashen da ke nahiyar su amfana.

Yanzu haka dai burin Michael Piontek shi ne ganin an fara amfani da wannan rigakafi wanda aka yi a garin nan na Langenfeld da ke yammacin Jamus daga nan zuwa tsakiyar shekara ta 2021 da muke shirin shiga, hakan kuma ya sanya da dama musamman a Asiya da Afirka na zuba idanu don ganin yadda za ta kaya.