Annobar corona na ci gaba da kisa a duniya
March 20, 2020WHO ta ce sama da mutune 240,000 sun kamu da Corona a duniya, inda mutane 10,000 suka mutu. Italiya nan kan gaba na jerin kasashen da Corovaris ta fi barna a cikinsu inda mutane 3433 suka mutu tun bayan bullarta. a Iran kuwa, an samu karin mutuwar mutane 149, saboda haka adadin wadanda Corona ta kashe ya kai mutum 1433. A China kuwa, mutane 3,250 ne suka mutu ya zuwa yanzu, yayin da a Jamus mutane 44 ne suka kwanta dama yayin da dubu 15 300 suka fama da wannan cuta.
Sai dai kukomimin lafiya na duniya sun nuna damuwa game da kasashe mafiya talauci inda ba za a samu damar killace jama'a a gidajensu ba musmaman ma a kasashen Asiya da Afirka, inda ake da mutane miliyan dubu uku da ba su mallaki dabarun yaki da kwayar cutar Coronavirus ba.
Dan kasar Gabon da ya kamu da Corona ya rigamu gidan gaskiya, wanda kuma shi ne na biyu a Afirka kudu da hamadar Sahara da ya mutu baya ga mataimakiyar kakakin majalisar dokokin Burkina Faso.