1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Annobar corona ta dauki hankalin taron G7

Ramatu Garba Baba
May 5, 2021

Yayin da ake shirin karkare taron G7, an yi kira da a yi adalci a rabon allurar rigakafin cutar corona a tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki da kuma kasashen duniya masu tasowa.

G7-Gipfel in London
Hoto: Stefan Rousseau/AP Photo/picture alliance

A yayin da ake shirin kamalla taron kasashen duniya masu karfin tattalin arziki wato G7, batun kamanta daidaito a yakar annobar coronavirus zai kasance batun da mahalarta taron za su fi mayar da hankali a wannan Laraba. An dade ana zargin rashin yin adalci a kasafta rigakafin allurar inda kasashe marasa karfi suka sami kaso kalilan na rigakafin.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ma, ta yi wannan kira, a daidai lokacin da kasashe matalauta ke fama a yakin da suke da annobar, ta ce ya zama wajibi a rage wannan wagegen gibin da aka samu, don sai da haka, za a iya guduwa tare, don a tsira tare. Corona ta kama sama da mutum miliyan talatin a fadin duniya tun bayan bullarta a Disambar 2019.