1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Blinken ya gana da Bola Ahmed Tinubu

January 24, 2024

A cigaba da kokari na tara kawaye sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce kasar Amurka na shiri ta taimaka wa yankin Sahel sake ginin demokaradiyya da fuskanbtar matsalar rashin tsaro.

 Antony Blinken ya gana da Bola Ahme Tinubu
Antony Blinken ya gana da Bola Ahme TinubuHoto: Ubale Musa/DW

 Kama daga batun tsarozuwa juyin mulki, ko bayan tattali na arzikin al'ummar yankin da ke cikin ni yasu, kasar ta Amurka ba ta boye bukatar neman sauya da dama a daukaci na yankin Sahel. Kuma sakataren harkokin wajen kasar Antony  Blinken da ya gana da hukumomin Najeriya dai ya ce Amurka na shirin ta agazawa Najeriyar cikin annobar rashin tsaro da ingantar demokaradiya a tsakani na kasashen ECOWAS.

Blinken ya sha alwashin ganin an tabbatar da demokaradiyya a Afirka

Anthony Blinken da TinubuHoto: Ubale Musa/DW

 Ziyarar da ke zaman ta biyua cikin shekaru guda Hudu na mulkin Biden dai, na kara fitowa fili da rawar Njeriyar da ke da babban aikin kare demokaradiyar ECOWAS amma kuma a cikin rikicin rashin tsaro. Rashin na tsaro dai ne ke zaman na kan gaba cikin hujjojjin 'yan juyin mulki na kasashen Mali da Nijar da kila ma Burkina Faso. To sai dai kuma jami’in ya ce Amurka na da dabaru da yawa na taimaka wa Abujar fuskantar kalubalen da ke da girman gaske cikin kasar a halin yanzu.‚ ''Yana da muhimmanci mu taimaka wa kawayensu da ke kokarin yakar rashin tsaro. Muna aiki domin taimaka wa Najeriya, muna son mu taimaka wa kawayenmu na tafkin Chadi dopmin inganta karfin jami’an tsaronsu na tunkarar  rashin tsaro.''

Taimakon fasaha da dabaru na kimiyya da Amirka za ta bai wa Najeriya

Hoto: Ângelo Semedo/DW

Wannan zai hada da fasaha za kuma mu yi musaya ta bayanai da kuma dabarun sirri, da shawara, dama kallon daukacin dabarun da za su maida hankali ga samar da tsaro ga 'yan kasa, da nuna musu cewar jami’an tsaro na aiki domin ba su kariya. Da nuna musu sun damu da su, kuma suna shirin biya na bukatunsu. In ba mu manta ba abun da ke faruwa ke nan a cikin Nijar a karkashin mulkin Bazoum kafin ayi masa juyin mulki, abubuwa su yi matukar lalacewa yanzu. To sai dai kuma ko ya zuwa ina taimakon na Amurka ke iya tasiri a kokarin kai annobar rashin tsaron zuwa ga kushewa, sake farfado da demokaradiyyar Nijar daga dogon suma ya kuma dauki hankalin kasar ta Amurka.