1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Antony Blinken zai fara ziyarar aiki ta tsawon mako a Afirka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 22, 2024

Mr Blinken zai fara yada zango ne a tsibirin Cape Verde, sannan ya wuce zuwa Cote d'Ivore don jinjinawa shugaba Alassane Ouattara, kan yadda ya tabbatar da dimokuradiyya a kasarsa. Daga nan ne kuma zai zarce zuwa Angola

Hoto: Tiksa Negeri/AFP/Getty Images

A Litinin din nan ce sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai fara wata ziyarar aiki ta tsawon mako guda a nahiyar Afirka, a wani mataki na kara yaukaka dangantar siyasa da tsaro, sakamakon yadda ayyukan ta'addanci ke ci gaba da mamaye kasashen yankin Sahel.

Karin bayani:Antony Blinken ya yi tozali da Mahmud Abbas kan rikicin Hamas da Isra'ila

Mr Blinken zai fara yada zango ne a tsibirin Cape Verde, sannan ya wuce zuwa Cote d'Ivore don jinjinawa shugaba Alassane Ouattara, bisa irin yadda yake tabbatar da dimokuradiyya a kasarsa. Daga nan ne kuma zai zarce zuwa Angola.

Bayani:Blinken ya kammala ziyara a Gabas ta Tsakiya da Asiya

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa kasashen Afirka da dama na nuna damuwa da yadda Amurkar ta fi mayar da hankali kan yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Ukraine, da ma yadda shugaban Amurka Joe Biden ya gaza cika alkawarin ziyartar Afirka a shekarar da ta gabata, kamar yadda ya yi ikirari tun da farko.