1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Antony Blinken zai je Saudi Arabiya da Masar kan yakin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 19, 2024

Mr Blinken zai je Saudi Arebiya ranar Laraba, sai Masar ranar Alhamis, yana mai cewar baya ga batun tsagaita wuta, za su tattauna kara shigar da kayan agaji Falasdinu musamman yankin Gaza mai fama da tsananin yunwa

Hoto: AMER HILABI/AFP

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai ziyarci kasashen Saudi Arabiya da Masar a cikin makon nan, don tattauna yadda za a lalubo hanyoyin cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yakin Gaza. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Mathew Miller da yanzu haka ke kasar Philippines yana halartar taron Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da safarar miyagun kwayoyi, ya ce Mr Blinken zai je Saudi Arebiya ranar Laraba, sannan ya zarce zuwa Masar ranar Alhamis.

Karin bayani:Masar da Qatar za su jagoranci tattaunawar tsagaita wutar rikicin Gaza

Ya kara da cewa baya ga batun tsagaita wuta, kasashen za su tattauna yadda za a kara azama wajen shigar da kayan agaji Falasdinu, musamman yankin Gaza mai fama da tsananin yunwa. Tuni dai shugaba Joe Biden ya nemi firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya aike da tawagar wakilansa zuwa birnin Washington, don tattauna hanyoyin kaucewa kisan fararen hula a yankin Rafah da ke kudancin Gaza.

Karin bayani:Blinken ya fara sabon rangadi a Gabas ta Tsakiya

Mr Biden ya sanar da hakan a shafinsa na X, yana mai cewar wannan wani mataki ne na takaice mace-macen fararen hular da ba su ji ba su gani ba a yakin da Isra'ila ke yi da mayakan Hamas.

Karin bayani:Antony Blinken ya yi tozali da Mahmud Abbas kan rikicin Hamas da Isra'ila

Mr Biden ya ce lokaci ya yi da za a cimma yarjejeniyar tsagaita wutar rikicin Gaza tare da sakin fursunonin da Hamas din ta yi garkuwa da su, bayan harin da ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara, lamarin da ya janyo kasashen yamma ciki har da Jamus ayyana ta a matsayin ta 'yan ta'adda.