APC: Bashin Najeriya ya kai kasafin kudin shekaru 2
May 19, 2015Wata sabuwar matsalar da ke iya kara tarnaki ga limaman sauyin dai na zaman gadon bashin da suke shirin yi daga gwamnatin PDP mai shirin yin adabo da gadon mulki. Gwamnatin kuma da ta gaji bashin trilliyan kusan uku da rabi a farkon fari, amma kuma ke shirin barin sama da trilliyan na Naira har guda takwas zuwa wa'adin karshe.
Ko a banan dai akalla Naira Miliyan dubu 930 ne dai gwamnatin da ke barin gadon ta ware da nufin biyan uwar kudi dama ruwa na basuka daban-daban da ke kan kasar. Adadin kuma da ke zaman kaso kusan 25 cikin 100 na daukacin kasafin kudin kasar na shekarar da ta lula ya zuwa yanzu.
To sai dai kuma sabon adadin bashin da ke zaman mafi girma a cikin gida a tarihin kasar da kuma ya kai kusan kasafin kudin na shekaru biyu dai na da tada hankali a tunanin Dr Nazifi Abdullahi Darma da ke zaman masanin tattalin arzikin kasar da ke da muradun sauyi yanzu.
Ko ma a ina aka kai ga jefa rara ta arzikin kasar ta Najeriya dai tun daga farkon watan janairun da ya shude ne dai mahukuntan kasar suka fara fadin sun dau yar bashin da nufin iya biyan albashin ma'aikata dama ragowar aiyuka na yau da kullu yaumin. Abun kuma da aka rika ta'allakawa da irin wadakar da ta biyo yakin neman zaben kasar da ya shude. Ya zuwa tsakiyar Mayun da muke ciki dai akalla jihohi 26 a cikin 36 sun gaza ga kokari na biyan ma'aikatan balle ragowar harkokin jama'ar da suka dora amana a bisa hannunsu. Abun kuma da ke nuna irin jan aikin da ke gaba a tsakanin kowa a kasar da ta dauki lokaci tana wadaka amma kuma ke neman rushewa a cikin kiftawar ido da bismilla.
To sai dai kuma a tunanin Dr Kole Shettima da ke zaman shugaban cibiyar demokaradiya da ci gaba mai zaman kanta cikin kasar, mafita na ga tsuke bakin aljihu da ma shugabancin koyi a bangaren 'yan sauyin da ke shirin kama kasar a cikin kasa da tsawon makonni biyun da ke tafe.
Kokari na rushe dadi ko kuma kokari na gyara na kasa dai, koma ya zuwa wane zango shugabanni na kasar ke iya hakuri da wadatar kai da nufin tabbatar da sake dora kasar bisa turba dai, ko a bana ana zargin majalisun kasar biyu da bai wa kasafin tsabar kudi har Naira Miliyan dubu 150 da nufin manya na aiyyukan da basu wuci sauyin motoci da gidajen kwana ba. Abun kuma da ke nuna alama ta tsohuwar al'adar masha'a a cikin guguwar sauyin dake kadawa yanzu.
To sai dai kuma a tunanin Hon Ahmed Babba Kaita da ke zaman dan majalisar wakilai daga katsina sauyin na zaman na wajibi kan kowa kama daga su kansu masu takama da yin dokoki ya zuwa talakawan da ke bukatar sauyin a kasa. Abun jira a gani dai na zaman makama ga masu alkawarin yin sauyi cikin kasar da tattalin arzikinta ke cikin wani hali yanzu.