1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APC ke kan gaba da yawan kuri'u a zaben Najeriya

Yusuf BalaMarch 31, 2015

A jihar Rivers da ake takaddama kan sakamakonta ya zuwa yanzu shugaba Jonathan ke da yawan kuri'u kan abokin karawarsa Muhammad Buhari.

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler


Jagoran jam'iyyar APC mai adawa a Najeriya Muhammad Buhari cikin sakamakon da ake bayyanawa yanzu haka a Najeriya shi ke kan gaba da kuri'u masu rinjaye sama da miliyan biyu kan abokin karawarsa shugaba mai ci Goodluck Jonathan, bayan da a yau Talata ta bayyana cewa Muhammad Buhari ke kan gaba da yawan kuri'u da aka samu a sakamakon da ya fita daga jihar Legas wacce ke zama daya daga cikin jihohi masu muhimmanci a zaben kasar.

Buhari dan shekaru 72 da ke takara a karo na hudu a zaben kasar ta Najeriya, ya fara da yawan samun kuri'un ne tun bayan da ya kankame wasu daga cikin jihohin arewacin kasar wadanda ke da mafi rinjayen Hausawa da Fulani Musulmi wato yankin da ya fito.

Tuni dai hukumar zabe mai zaman kanta a kasar ta Najeriya ta fara shan suka daga bangaren jam'iyyar PDP mai mulki, inda ta bayyana cewa yadda hukumar ta ke bayyana sakamakon akwai kumbiya-kumbiya a cikinsa.

A jihar Rivers da ake takaddama kan sakamakonta ya zuwa yanzu shugaba Jonathan ke da yawan kuri'u kan abokin karawarsa Muhammad Buhari inda Jonathan ke da sama da kashi 94 cikin dari.

Nan gaba a yau ne dai ake saran bayyanar sakamako na karshe kan wanda ya yi nasara a zaben kasar ta Najeriya da aka fara tun daga ranar Asabar da ta gabata.