APC na fuskantar kalubale a Arewa yayin da zabe ke kara karatowa
October 22, 2026
Tun daga shekarar 2015, yankin arewacin Najeriya ya kasance daya daga cikin manyan sansanonin goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki. A zaben shugaban kasa na 2023 ma, yankin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya samu kaso mai yawa na kuri'unsa daga arewa.
Sai dai yayin da ake tunkarar babban zaben 2027, alamun damuwa na kara bayyana kan makomar jam'iyyar a yankin da ya kasance ginshikinta tsawon shekaru.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na cewa jerin rikice-rikicen cikin gida da ke addabar APC a wasu jihohin arewa, ciki har da Kano da Katsina da Benue da Kwara. Wadannan sabanin ra'ayoyi da rikice-rikicen shugabanci na kara haifar da tambayoyi kan hadin kan jam'iyyar a yankunan da suka kasance maboyarta.
Baya ga rikicin cikin gida, APC na kuma fuskantar kalubalen sabbin kawance tsakanin jam'iyyun adawa da wasu fitattun 'yan siyasa a jihohi irin su Kebbi, Benue da Gombe. Wasu na ganin irin wadannan kawance na iya rage tasirin jam'iyyar idan ba a dauki matakan da suka dace ba.
Haka kuma, alamu na nuna cewa wasu daga cikin magoya bayan da suka kasance sahun gaba wajen mara wa APC baya a baya sun fara nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al'amuran mulki, musamman dangane da kalubalen tattalin arziki da tsadar rayuwa.
Masu lura da al'amuran siyasa sun ce jam'iyyar na kuma fuskantar matsin lamba daga wasu sarakunan gargajiya da malaman addini, wadanda a baya ake kallonsu a matsayin manyan abokan tafiyarta a yankin.
Yayin da siyasar 2027 ke kara tasowa, tambayar da ake yi ita ce ko APC za ta iya shawo kan wadannan kalubale tare da ci gaba da rike farin jininta a arewacin Najeriya, ko kuwa yankin zai fuskanci sabon salo na siyasa da zai iya sauya taswirar zaben kasar.