1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

APC za ta fitar da dan takara a zaben 2023

Abdoulaye Mamane Amadou
June 7, 2022

A wannan Talatar ce ake sa ran jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zabi wanda zai kasance mata dan takara a babban zaben shugabancin kasar da za a yi a watan Fabrairun badi.

Arfika Nigeria APC Abuja
Hoto: Ubale Musa/DW

Fiye da wakilai dubu biyu da 300 ne ake sa ran su halarci babban birnin tarayyar Najeriya Abuja don tantance daya daga cikin mutun 23 da ke sha'awar jam'iyyar APC ta tsayar da su takara a zaben na 2023 a kasar da ta fi kowace yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Nan da 'yan mitoci kalilan ne dai ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari ya kasance a dandalin Eagle Square don halartar bikin zaben dan takarar, kana ana dakon samun sakamakon zuwa karshen wannan dare.

Jam'iyyar PDP mai adawa da ke zama babbar abokiyar hamayyar APC mai mulkin Najeriya tuni ta tsayar da nata dan takara, inda ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dantakarta a zaben na Najeriya, kasar da wasu alkaluma suka ce na da kimanin mutun miliyan 83 da ke fama da tsabagen talauci da fatara daga cikin mutun miliyan 215 na al'ummar kasar.