Ranar juyin-juya hali a Masar
January 26, 2015Talla
Wannan dai shi ne karo na hudu da aka yi wannan buki da ke tunawa da juyin-juya halin kasar da ya kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak a shekara ta 2011. Arangama mafi muni ta faru ne a unguwar Matariya da ke birnin Alkahira, unguwar da ke zaman matattarar 'ya'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi da ke goyon bayan hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi. Kungiyar kuma da tun bayan kifar da Morsin take gwagwarmayar ganin an dawo da shi kan mukaminsa ba tare da ta cimma nasara ba.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal