1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangama tsakanin 'yan sandan Masar da masu bore

Charles Duguid PenfoldFebruary 3, 2012

Rigimar da ta biyo bayan salwantar rayukan mutane kimanin 75 a filin ƙwallo na Port Said na ci gaba da yaɗuwa i zuwa wasu birane na ƙasar Masar.

A soccer fan flees from a fire at Cairo stadium February, 1, 2012. Crowds set parts of the stadium on fire in reaction to a soccer pitch invasion during another soccer match held at the Egyptian city of Port Said. At least 50 people were killed and hundreds of others injured on Wednesday after a soccer pitch invasion in Port Said, healthy ministry sources said, in an incident that one player described as "a war, not football". REUTERS/Stringer (EGYPT - Tags: SPORT SOCCER CIVIL UNREST)
Rikicin ya samo tushe a filin ƙwallo na Port Said.Hoto: Reuters

Mutane biyu sun rasa rayukansu a birnin Suez na ƙasar Masar lokacin da 'yan sanda suka yi amfani da bindiga wajen tarwatsa zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin mulkin soje. A Alƙahira babban birnin ma, masu boren sun shafe tsawon dare suna fito na fito da 'yan sanda, da nufin nuna ɓacin ransu game da kamun ludayin hukumomin soje akan arangamar ranar laraba da ta salwantar da rayukan mutane aƙalla 75 a filin ƙwallon na Port Said.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da borkonon mai sa ƙwalla domin hana masu boren kutsawa cikin ma'aikatar cikin gidan ƙasar Masar. An ruwaito cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ta harbi jami'an tsaro da duwatsu.

Kanfanin dillacin labaran Masar ya bayyana cewa kimanin mutane 400 suka jikata a halin yanzu. sai dai kuma zanga-zangar ta yaɗu i zuwa birnin Port said inda dama a can ne rikicin ya samo tushe. Masu zanga-zangar sun zargi hukumomi da rashin ɗaukan matakan rigakafi domin hana ɓarkewar arangama da ta haddasa mutuwar mutane da dama .

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza sadissou Madobi