1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangamar Isra'ila da Falisdinawa

December 28, 2011

Isra'ila ta yi luguden wuta akan zirin Gaza a matsayin martaninta ga hare-haren rokokin da ta fuskanta daga mayakan Falisdinu

A woman uses her phone to take a photograph at a site where a rocket fired from the Gaza Strip hit Ashdod, southern Israel, Saturday, Oct. 29, 2011. Israeli aircraft struck at Palestinian militants on Saturday who responded with a volley of rockets which rained on southern Israeli towns, Israeli and Palestinian officials said. Palestinian sources said that seven militants were killed while the Israelis reported several civilians injured. (Foto:Ariel Schalit/AP/dapd)
Harin Isra'ila akan GazaHoto: dapd

 An sake samun dauki-ba-dadi tsakanin Isra'ila da mayakan Falisidinu wanda a cikinsa Isra'ila ta yi luguden wuta sau biyu a zirin Gaza. Likitocin masu ba da taimakon gaggawa a yankunan Falisdinawa sun ce mutun daya ya mutu wasu kuma su 12 sun samu raunuka. Ma'aikatar sojin Isra'ila ta jadadda cewa wani rukuni na 'yan ta'adda da ka iya shirya kai hare hare akan iyakar Isra'ila da Masar da ke yankin Sinai ne aka nufa da wannan harin. A ranar Litinin 26-12-2011 Falisdinawa su harba roroki guda biyu  zuwa cikin kudancin Isra'ila. To ama babu wanda ya mutu ko ya samu rauni.

 Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu