1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangamar Kurdawa da jami'an tsaron Turkiyya

September 3, 2012

Mutane 29 suka hallaka a dauki ba dadi tsakanin 'yan tawayen Kurdawa da jami'an tsaron Turkiyya a lardin Sirnak.

Turkey sent a convoy of about 20 vehicles carrying troops, missile batteries and armoured vehicles to the border with Syria. The convoy left a base in Gaziantep province to head south to Kilis province, where the troops will stay, the state-run Anatolian news agency said. That area, which has a large Kurdish population, has been spared much of the violence seen elsewhere in Syria, but Turkey is worried the PKK could exert influence there amid a power vacuum and threaten Turkish security at the border. The PKK has waged a 27-year campaign for autonomy in Turkey's largely Kurdish southeast, and more than 40,000 people, mainly Kurds have died in the conflict. Photo by Muslum Etgu/AA/ABACAPRESS.COM # 329205_002 pixel
Hoto: picture alliance/abaca

Wasu mayakan 'yan tawayen kurdawa dauke da manyan makamai da kuma gurneti suka kaddamar da hari akan wani ginin jami'an tsaron Turkiyya cikin dare, lamarin daya janyo mummunanr taho mu gamar da ta haddasa mutuwar mutane 29. A cewar Vahdettin Ozkan, gwamnan lardin Sirnak, inda lamarin ya afku, jami'an tsaro tara ne suka mutu yayin da wasu takwas kuma suka sami rauni a lokacin taho mu gamar. Wasu majiyoyi daga yankin kuma su bayyana cewar kimanin kurdawa 'yan tawaye 20 ne suka mutu sanadiyyar bata-kashin baya bayannan daya gudana a tsakanin 'yan tawayen PKK da hukumomin na Turkiyya suka haramta da kuma dakarun gwamnati. A 'yan kwanakin baya bayannan dai 'yan tawayen na PKK sun tsaurara farmakin da suke kaddamarwa akan jami'an tsaron Turkiyya, inda kafofin yada labaran cikin gidan Turkiyya da ma jami'an gwamnatin kasar ke dangantaka hakan da rikicin da ke ci gaba da wanzuwa a kasar Siriya da ke makwabtaka da ita Turkiyya. Firayi ministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi barazanar daukar matakin soji muddin dai 'yan tawayen suka samar da sansani a cikin kasar Siriya.

Mawallafi:  Saleh Umar Saleh
Edita:   Abdullahi Tanko Bala