1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Armeniya da Azerbaijan sun yi sulhu

November 10, 2020

Kasashen Armeniya da Azerbaijan sun sanya hannu a kan yarjejeniyar sulhu bisa jagorancin kasar Rasha kan rikicin da suke fafatawa kan yankin Nagorno-Karabakh.  

Aserbaidschan-Armenien | Konflikt in Berg-Karabach
Hoto: Iliya Pitalev/Sputnik/dpa/picture alliance

Sai dai kuma yarjejeniyar ta bar baya da kura inda ta haifar da bore a Armeniya.

Daruruwan masu zanga zanga sun yi dandazo a Yeranvan babban birnin kasar tare da afkawa ofisoshin gwamnati.

Masu zanga-zangar sun kuma shiga majalisar dokoki inda suka yi kira ga firaministan kasar Nikol Pahiyan da ya yi murabus.