1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArmeniya

Armeniya da Azerbaijan sun cimma daidaito kan rikicin iyaka

May 16, 2024

Armeniya da makwabciyarta Azerbaijan sun cimma yarjejeniya kan wani bangare na iyakokinsu a wani mataki na sake daidaita dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Armeniya da Azebaijan sun cimma daidaito kan rikicin iyaka
Armeniya da Azebaijan sun cimma daidaito kan rikicin iyakaHoto: KAREN MINASYAN/AFP

Bayan share gwamman shekaru ya yake-yake da takadddama sun yanke shawarwar saka hannu kan yarjejeniyar da ta raba wani bangare na iyakokin kasashen biyu. 

Armeniya da Azerbaijan dai sun gwabza yaki a karo biyu kan 'yancin mallakar yakin Nagorno-Karabakh, kafin daga bisani a watan Satumban bara Azerbaijan ta kaddamar da wani gagarumin farmaki domin fatattakar jagororin Armeniya da suka share shekaru 30 suna fafutukar ballewar yankin.

Karin bayani: Taron sulhu tsakanin Armenian da Azerbaijan

A cikin wata sanarwa da kasashen biyu suka fidda a ranar Alhamis 16.05.2024, sun ce sun cimma matsaya kan wani bangare na iyakarsu bisa tanadin wata tsohuwar taswira tun ta lokacin da kasashen ke karkashin Tarayyar Soviet.

Sabuwar yarjejeniyar ta tanadi cewa wasu kauyuka hudu da ke kan iyakar kasashen biyu za su fita daga hannu Armeniya domin komawa karkashi ikon Azerbaijan.

Karin bayani: Kokarin sasanta Armeniya da Azerbaijan

Tuni ma firaministan Armeniya Nikol Pachinian ya yaba da wannan mataki yana mai cewa a karon farko tun bayan samun 'yancin kai daga Tarayyar Soviet an yanka iyakokin kasar a hukumance.