1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Armeniya na neman tallafin EU

September 30, 2023

Armeniya na neman agaji daga kungiyar Tarayyar Turai yayin da 'yan gudun hijira daga yankin Nagorno-Karabakh ke ci gaba da kwarara zuwa kasar.

Al'ummar yankin Nagorno-Karabakh na tserewa yankin zuwa Armeniya
Al'ummar yankin Nagorno-Karabakh na tserewa yankin zuwa ArmeniyaHoto: SIRANUSH ADAMYAN/AFP/Getty Images

Kusan dai dukkanin mazauna yankin ne da rikici ya daidaita suka kaura zuwa Armeniya. Offishin Firanministan Italiya ya sanar da cewa, Armeniyar ta bukaci tallafin EU na samar mata da tallafin magunguna da sauran kayayyaki na wucin gadi.

Karin bayani:Nagorno-Karabakh: Al'umma na neman agaji 

Offishin ya kara da cewa, gwamnatin Rome na yi dukannin me yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya a yankin na Nagorno- Karabakh.

Alkalumma Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da cewa, kawo yanzu kimanin zauna yankin dubu 100 daga cikin dubu 120 ne suka tsere zuwa Armeniyar bayan da Azerbaijan ta kai farmakin sake kwace ikon yankin.