1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gumurzu tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda

Uwais Abubakar Idris AH
August 5, 2024

A Najeriya an shiga yini na biyar na zanga-zangar tsadar rayuwa inda jami'an tsaro ke ci gaba artabu da masu zanga-zangar inda a wasu wuraren suka yi harbe-harbe.

Hoto: Kola Sulaimon/AFP

 Tirjiyar dai ta karu ainun domin matasan sun fito fiye da sauran ranakun da suka yi suna wannan zanga-zanga da ta shiga yini na biyar, kama daga jihohin Kaduna, Katsina Kano da ma Lagos cibiyar kasuwancin kasar. Mr Deji Adeyanju yana cikin wadanda ke jagorantar matasan da ke zanga-zangara a Najeriya. ‘'Abin da ya sanya mutane ke ci gaba da fitowa zanga-zanga shi ne shugabaninmu ba sa ma kokari ba su nuna cewa sun damu da halin da jama'a suke ciki, yanzu ga maganar da ake yi ga rashin abninci ga yunwa ga rashin tsaro, amma sai 'yan sanda suka zo suna ta harba barkonon tsohuwa har sun kashe mutane da yawa a Najeriya. Ni a ganina ya kamata gwamnati ta saurari halin da mutane suke ciki''.

Hoto: Benson Ibeabuchi/AFP

Zargi na nuna karfinda ya wuce iyaka da ake yi wa jami'an tsaron Najeriyar inda a wurare da dama ta kai su ga amfani da harsashi a kan fararen hula da ya yi dalilan raunawa da ma kashe jama'a. Tuni kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International ta kai ga sanya baki tare da jan hankalin gwamnatin Najeriya a kan illar da ke tattare da wannan hali da ake ciki. Mallam Isa Saanusi shi ne daraktan kungiyar a Najeriya. ‘'Abin takaici ne cewa an yi asarar rayuka tun daga ranar 1 ga watan Augusta har zuwa yau, a fili yake cewa jami'an tsaro sun yi amfani da karfin da ya wuce kima a wanda ya zarta abin da doka ta ce a yi, sun bude wuta sun harbe mutane wannan bai dace ba, don haka gwamnati ta  tsawata ta kuma yi bincike don a tabbatar da cewar an yi hukunci''

Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Ala'marin dai da ya sake rincabewa a Jihar Kaduna inda gwamnati ta sanya dokar hana fita ta saoi 24 a birnin Kadauna da Zaria saboda artabun tsakanin masu tirjiya da jami'an tsaro. Alhaji Abdulrrahman Kwacham shi ne shugaban kungiyar ci gaban yankin arewa maso gabashin Najeriya. '' Duk da barnar dukiya da asarar rayyukan jama'a a sakamakon zanga-zangar matasan na dagewa kan cewa sai sun kwashe kwanaki goma suna fafatawa abin da ke nuna da sauran aiki a gaba''.An ci gaba da mumunan artabu a tsakanin matasan da ke zanga-zangar tsadar rayuwa da jami'an tsaron Najeriyar a mafi yawan sassan kasar inda aka ga fitowar matasan da ke nuna tirjiya ga  gwamnati.

Hoto: Marcus Ayo/AP/picture alliance
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani