1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sojoji sun kashe 'yan Shi'a da dama

Uwais Abubakar Idris AH
October 30, 2018

A Najeriya a rana ta uku a jere ‘yan Shia sun sake yin tataki tare da shan arangama da jami’an tsaro a Abuja fadar gwamnatin.

Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Tatakin da 'yan kungiyar ta Shi'a ke yi a Abuja ya sanya daukan tsauraran matakai a daukacin hanyoyin shiga da fita Abuja, amma duk da haka sai dai ta kai ga artabu tsakaninsu da jami'an tsaro, wanda ya fi muni shi ne abin da ya faru a unguwar Nyanya da ke Abuja inda ta kai ga sojojin bude wuta a kansu, mutane dai da dama sun mutu kana wasu suka jikkata.

Alkaluman yawan mutanen da aka kashe a artabun da aka yi na sabawa juna, saboda rashin sanin zahirin adadin da abin ya shafa, musamman wadanda suka mutu. Masana harakar tsaro da ma kare hakin jama'a na nuna damuwa a kan daukacin lamarin da jami'an tsaro suka yi gum a kan bayyana halin da ake ciki.