1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asarar rayuka a zanga-zangar Yukren

Jane McintoshFebruary 19, 2014

A kalla mutane sama da 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta rikide ta koma zuwa tashin hankali a kasar ta Yukren.

Hoto: Reuters

Baya ga asarar rayukan dai mutane sama da 200 kuma sun jikkata a kokarin da jami'an tsaron Yukren din ke yi na fatattakar masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ke ci gaba da yin zaman dirshan a dandanlin 'yanci dake Kiev babban birnin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron kasar ta Yukren sun cinna wa tantunan da 'yan adawar suka kakkafa a dandalin 'yancin na Kiev wuta, yayin da su kuma suka mayar da martani da bama-bama na man fetur. Bayan ganawar da ya yi da Shugaba Viktor Yanukovych jagoran 'yan adawar kasar Vitali Klitschko ya bukaci jami'an tsaron da su janye daga dandalin 'yancin yana mai cewa:

"Mutun guda ne kawai zai iya gyara kan abin da ke gudana a yanzu haka, ina yin kira ga shugaban kasar Ukraine. Dukkan nauyi da kuma mulki yana hannunsa, shi kadai ne zai iya magance wannan matsalar. Ya kamat ya sanya ranakun da za a gudanar da zabukan 'yan majalisa da kuma shugaban kasa, domin hakan shi ne kadai mafita".

A nasa bangaren da yake ganawa da jagororin 'yan adawar kasar Shugaba Yanukovych, bukatarsu ya yi da su nisanta kansu da masu yin ko wace irin zanga-zanga a kasar, yayin da a hannu guda kuma kasashen duniya ke ci gaba da nuna damuwarsu kan halin da ake ciki a kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal