Mamakon ruwan sama da aka yi ya haifar da ambaliyar ruwa a kanana hukumomi 17 da ke jihohin Borno da Yobe, inda ya lalata dubban gidaje da makarantu da kasuwanni da kuma Gonaki.
Talla
Tuni dai gwamnatocin jihohin na Yobe da Borno, suka dauki matakin kai dauki ga wadanda bala'in amlabiyar ruwan ta shafa. Jihohin Arewa maso gabashin Najeriya na shaida ganin ibtila'in ambaliyar ruwa a wannan lokaci, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi tare da gurgunta harkokin sufuri da noma da ma kasuwanci. Manyan hanyoyi da su ka hada shiyyar da sauran sassan Najeriyar kamar muhimmiyar hanyar da ta hada jihohin Borno da Yobe da Bauchi da bangaren jihohin Arewa maso Yammacinkasar, ta yanke saboda ambaliyar da aka yi a wani yanki na jihar Bauchi.
Daga Najeriya zuwa Pakistan, ambaliyar ruwa na tagayyara al'umma a duniya
Mutane fiye da 600 suka rasu a ambaliya a Najeriya yayin da wasu dubbai suke jiran taimakon jinkai. Ambaliyar ta shafi jihohi 33 daga cikin 36, ta jefa kasar cikin hadarin jinkai kama daga cutattuka zuwa karancin abinci. Ana yawan samun ambaliya a yankunan kasar na gabar kogi, amma wannan ita ce mafi muni a cikin fiye da shekaru goma.
Hoto: Ayodeji Oluwagbemiga/REUTERS
Ambaliyar ruwa ta saukin fari a in Chad
Bayan tsawon lokaci na fari, ruwan da aka dade ba a ga irinsa ba cikin shekaru 30 ya sa yankuna da dama sun zama gulbi a kasar Chadi. Dubban mutane sun yi kaura, makiyaya suka rasa inda za su ciyar da dabbobinsu. Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kiyasin fari da ambaliya sun sa mutane fiye da miliyan biyu cikin kangin yunwa yayin da farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi.
Hoto: Mahamat Ramadane/REUTERS
Ruwa ya mamaye Sri Lanka
A kalla mutane uku sun mutu a ambaliyar ruwa a Sri Lanaka, inda lamarin ya fi kamari a Colombo babban birnin kasar. Ambaliyar ta jefa sassan kasar cikin mummunan hadari, yayin da ake hasashen samun karin ruwan sama mai yawa a 'yan kwanaki masu zuwa.
Hoto: Pradeep Dambarage/NurPhoto/picture alliance
Pakistan na fuskantar cutattuka da tamowa
Ambaliyar ruwa ta sa mutane fiye da 500,000 zama a cikin tantuna a fadin Pakistan, wasu mutanen fiye da 1,700 sun rasu. Ambaliyar na raguwa amma mutanen da abin ya shafa a yankuna kamar Sindh da Balochistan a yanzu suna fuskantar hadarin yaduwar cutattukan da ake samu daga ruwa saboda lalacewar asibitoci, da karancin magunguna da kuma rashin bandakuna.
Hoto: Sabir Mazhar/AA/picture alliance
Zaftarewar kasa ta rufe garuruwa a Venezuela
Zaftarewar kasa sakamakon ambaliya da kuma tumbatsar koguna a Venezuela sun haddasa mutuwar mutane 50. Gwamnatin kasar ta ce ruwan sama mai yawa ya haifar da bala'i mafi muni a kasar wanda ba a ga irinsa ba cikin shekaru goma, inda ta dora alhakin hakan a kan sauyin yanayi. Ana hasashen samun karin ruwan sama a fadin kasar da suka hada da jihar Aragua da ambaliyar ta yi mummunan ta'adi.
Hoto: Pedro Rances Mattey/AA/picture alliance
Ambaliyar ruwa zahirin rayuwa Philippines
A yankunan Philippines, 'yan Achaba sun fara sauya fasalin baburansu domin dacewa da yanayin da aka shiga na ambaliya. A Hagonoy da ke wajen babban birnin Manila, zurfin ruwan ya kai kimanin mita biyu a lokacin damuna. A farkon wannan makon, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya shafe kauyuka da gonaki a fadin arewacin kasar.
Hoto: Eloisa Lopez/REUTERS
Shin laifin sauyin yanayi ne?
Munanan lamuran yanayi suna yawan faruwa akai akai saboda mutane da suka haddasa sauyin yanayi. Yanayi da iska mai zafi kan rike ruwa da zai iya kwararowa a matsayin ruwan sama. Yayin da ba za ka iya fadin yawan sauyin da ke taimakawa kowane yanayi ba, amma lamarin a baiyane yake. Kuma kasashen da suka fi fuskantar matsalar sune kuma suka fi saukin haddasa ta.
Hoto: Sanjev Gupta/dpa/picture alliance
Me duniya za ta iya yi a game da wannan?
Domin tsawa kan yarjejeniyar Paris kan sauyin muhalli, kasashe na bukatar rage fitar da hayakin masana'antu zuwa tsakiyar karni. Kasashen da suke fuskantar hadari kuma suna bukatar samar da matakan fadakarwa kan ambaliya domin rage tasirin bala'oi da suka shafi muhalli. Samar da kudaden aiwatar da irin wannan tsari shi ne zai kasance babban batu a taron sauyin yanayi da ke tafe.
Hoto: Branden Camp/AP Photo/picture alliance
Hotuna 81 | 8
Yanzu haka a jihar Yobe bayan lalata gidaje ambaliyar ta kuma lalata gonaki tare da lalata hanyoyi, abin da ya sa al'ummomi da dama suka kauracewa matsugunansu zuwa wuraren da hukumomi suka samar ga mutane. Haka wannna matsala take a jihar Borno, inda nan ma aka samu rubtawar gidaje da lalacewar gonaki saboda matsalar ta ambaliya. Ana dai bayyana fargabar barkewar cututtuka, sakamakon wannan ibtila'i. Sai dai hukumomi na cewa suna bakin kokarinsu, domin taimakon wadanda ambaliyar ta shafa. Masu yaki da gurbatar muhammali na kira ga hukumomi su karfafa aikin fadakar da al'umma kan hadarin lalata muhammali, wanda shi ne ke haifar da irin wannan abaliyar ruwan ko za a samu saukin matsalar a nan gaba.