Ashton na ziyarar Gabas ta Tsakiya
July 17, 2010Babbar jami'ar harakokin diplomasiyar ƙungiyar Tarayyara Turai Catherine Ashaton ta fara ziyarar kwanaki ukku a yankin Gabas ta Tsakiya ciki kuwa har da kai ziyara yankin zirin Gaza da Isra´ila ta killace.
A lokacin wannan ziyara ana fatan Ashton zata gana da shugaba Mahmud Abbas a yau Asabar, kana a gobe ta ziyarci zirin Gaza. Wannan dai ita ce ziyarar ta farko a yankin tun bayan harin da sojojin Isra´ila suka kai akan ayarin jiragen ruwan kayan agajin ga Palaɗinawan Gaza da ya kashe mutane tara, harin da kuma ya jawo wa Isra´ilan tofin Allah tsine daga ƙasashen duniya da dama.
A wata sanarwa da ta fitar, Ashton ta ce ƙungiyar EU ta shirya gabatar da wani ƙudiri da zai samar da mafita game da takunkumin da Isra´ila ta ƙaƙabawa yankin na Gaza wanda ke ƙarƙashin mulkin gwamnatin Hamas mai kishin addinin Islama.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Yahouza Sadissou Madobi