1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asia Bibi 'yar Pakistan ta fice daga kaso

Yusuf Bala Nayaya
November 8, 2018

Asia Bibi, Kirista da ake zargi da batanci ga addinin Islama ta bar gidan kaso, kamar yadda kafafan yada labarai suka nunar.

Asia Bibi
Hoto: Getty Images/AFP/M. Bureau

Bibi da kotun koli ta sallama a makon da ya gabata, bayan da fari an yanke mata hukuncin kisa saboda batanci ga addinin Islama ta fice daga gidan kaso kamar yadda wasu kafafan yada labarai na kasar ta Pakistan suka ba da labari a ranar Laraba.

Wasu rahotanni na kafafan yada labaran sun yi nuni da cewa da alama matar bayan fita daga gidan kason ta kama hanya ce ta ficewa daga kasar ko da yake gwamnatin kasar ta Pakistan ba ta tabbatar da hakan ba.

Har ila yau akwai rade-radin cewa an umarci iyalanta su zauna cikin shirin ficewa daga kasar ta Pakistan. Ba a dai kai ga ba da tabbaci ba na ficewar ta Asia Bibi ko tana cikin Pakistan sai dai Antonio Tajani shugabar Majalisar Tarayyar Turai ya ba da tabbacin cewa Bibi ta fita daga gidan kaso, kuma ba da dadewa ba ne za su gana da ita tare da iyalanta a majalisa kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.