1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafar Intanet ta tona asirin sojin Sudan

Mahmud Yaya Azare GAT
July 15, 2019

A kasar Sudan matakin mahukuntan kasar na dawo da Intanet ya jawo yin tonon silili ga irin aika-aikar da sojoji suka tafka kan fararen hula a tsukin lokacin da aka katse da yanar gizo a kasar.

Sudan Soldaten RSF
Hoto: picture-alliance/Photoshot/M. Babiker

Gwamman hotuna da bidiyo ne aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta da yanar gizo kan abin da ya yi ta faruwa a kasar ta Sudan a tsukin lokacin da sojojin suka katse yanar gizo a fadin kasar ta Sudan, musamman a ranar da aka fasa zaman dirshan din masu fafutuka, yadda ake iya ganin wasu sanye da kayan sarki na bude wuta kan farar hular da ba su rike da ko da tsinke, wani kwamandan sojojin kuma na ba su umarnin harbi kan mai uwa da wabi, kai hatta ko da bisa gawa ne. A wasu hotunan kuma ana iya ganin yadda wasu sanye da kayan sarkin na duka da tattaka wasu mutane shanye a rana, suna tilasta musu jinjina wa tsarin mulkin soji da tsine wa tsarin farar hula.

Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Tuni dai kungiyar kare hakkin dan Adam ta nemi da a gudanar da bincike mai zaman kansa don gurfanar da su gaban kuliya.
A baya dai Shugaban Majalisar Wucin Gadin Abdulfattah Burhan ya fito karara ya nesanta rundunar sojin kasar da aikata wannan aikin ta'asar. To sai dai wani faifayin bidiyo da ake ta yadawa a shafukan sada zamunta tun bayan kotun kolin kasar ta tilasta wa kamfanonin yanar gizo da su daina toshe yanar gizon, na nuna yadda Kakakin Rundunar Sojin Nuridden Kabbashi yana ta da tsimin wasu sojojin da za su fasa zaman dirshan din, yana mai siffanta masu zaman dirshan din da miyagun lafuzza.
 
Hakan dai na wakana ne a daidai lokacin da ake samun tseko kan rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hada kan kasar, sakamakon dagewar da sojojin ke yi kan sai a sanya batun ba wa membobin Hukumar Sojin Wucin Gadi kariya ta shari,a ta din-din-din, batun masu fafutukarke adawa da shi.

Hoto: picture-alliance/AA