Aski ya kai gaban goshi kan ficewar Birtaniya daga EU
March 21, 2017Shugaban majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai EU, Donald Tusk ya sanar a wannan Talatar cewa zai kira wani taron kolin membobi 27 na kungiyar ba tare da Birtaniyya ba a ranar 29 ga watan Afrilu, inda za a tattauna game da ficewar Birtaniya daga EU. Tusk ya ce abinda za a ba wa fifiko shi ne samun tabbaci da kuma fayyace wa dukkan al'ummomin Turai da kamfanoni da kuma kasashe membobi wadanda ficewar Birtaniyar za ta shafa.
Ya ce: "A dangane da sanarwar da aka bayar ranar Litinin a birnin London, ina mai shaida muku cewa zan kira wani taron kolin kungiyar EU a ranar 29 ga watan Afrilu inda za mu amince da ka'idojin tattaunawar ficewar Birtaniya. Da na so a ce Birtaniya ba ta zabi ficewa daga EU ba, amma mafi rinjayen masu zabe a Birtaniya sun yanke hukunci na daban. Saboda haka za mu yi kokarin ganin illar da shirin rabuwar zai janyo kadan ce."
A ranar 29 ga watan nan na Maris Birtaniya za ta fara shirye-shiryen rabuwa da kungiyar EU, inda za a kaddamar da tattaunawa ta tsawon shekaru biyu tsakanin bangarorin biyu.