'Yan siyasa masu adawa da Biya sun gaza hada kawunansu
October 7, 2025
Duk da kokarin da wasu jam'iyyun adawa da masu fada a ji suka yi wajen kulla kawance da zai iya kayar da Paul Biya na ci tura, amma Bello Bouba Maigari da Issa Tchiroma Bakary na ci gaba da yin watsi da tayin.
'Yan takara Issa Chiroma Bakary na jam'iyyar FSNC da Bello Bouba Maigari na jam'iyyar UNDP sun kasance wa gwamnatin Paul Biya kadangaren bakin tulu. Dalili kuwa shi ne, dukkan su biyu sun fito daga Arewa da ke kusan kashi 40% na yawan kuriù da ake da su a Kamaru.
Sai dai sun kasa hada karfi da karfe domin tinkarar jam'iyyar RDPC da ke ci a yanzu, duk da goyon baya da suke samu daga wasu jam'iyyun adawa . Maimakon haka ma, suna musayar munanan kalamai da ke tsakaninsu, saboda kowa na ganin cewar shi ya fi dacewa da shugabancin kasa.
Aboubakar Saddat, mamba a kwamitin koli na jam'iyyar UNDP ya ce dan takararsu Bello Bouba Maigari na shirye wajen hada gwiwa bisa sharadin bai wa gwaninsu tikitin takara daya tilo ta ‚yan adawa
Bello Bouba Maigari da Issa Tchiroma Bakary sun yi aiki karkashin jam'iyya daya a lokacin da guguwar neman kafa jam'iyyu barkatai ta kada a Kamaru. Amma raba gari da suka yi ya haifar da gabar siyasa tsakaninsu, duk da cewa sun yi aiki tare a gwamnatin Paul Biya na tsawon shekaru da dama.
Mouhamadou Sabiou Inouwa, babban jami'in yada labarai da wallafe wallafe a yanar gizo na jam'iyyar FSNC ya ce dan takararsu Issa Tchiroma Bakary ba zai taba mika wa Bello kai domin bori ya hau ba.